Sustainability / Dorewar kafofin yada labarai masu zaman kansu

Ga mafi yawan sabbin kafafen yada labarai masu zaman kansu, kwakwarar dabara mai dorewa ta samun kudi ce kadai za ta ba su tabbacin cigaba da aikin da zai wuce shekaru biyu. Ga dai wadannsu daga cikin darussan da abokan aikin mu a kasashen duniya suka rubuta dangane da hanyoyin samun kudaden shiga, yanayin zama mamba, da gudanar da taruka, da hanyoyin samun kudi da sauran su

Sustainability: Overview/ Dorewar hanyoyin samun kudin tafiyar da kafafen yada labarai masu zaman kansu : Gabatarwa

Aikin jarida na masu zaman kansu ya cigaba da bunkasa a hanakali na tsawon shekaru 20 yanzu, bisa dalilan da aka riga aka yi bitansu, wadanda suka hada da mutuwar samfuran kasuwanci na gargajiya, da zuwan sauyi a yanayin fasahohi da ma yadda aikin jarida mai sahihanci ke samun tallafi duk da irin rikicin da ake gani a masana’antan aikin jaridar.

A wannan kundin, GIJN ta yi bincike kan irin dabarun da za su tabbatar da dorewar aikin jarida mai zurfi a kasashen duniya.

An ci sa’a yanzu ana samun karuwar wadanda ke bayar da tallafi ga aikin jarida. Wannan na samar da damammaki amma kuma yana bukatar dabaru na samun kudi dan tabbatar da dorewar kudin. Ga wadanda ke bayar da kudaden tallafi domin aikin jarida, hakan na janyo musu kalubale na musamman wadanda muka fayyace a sashen da muka kira “shawarwari ga masu bayar da tallafi.”

Bacin haka, kungiyoyin da ke aikin jarida dan samun riba, suna amfani da sabbin dabaru. Suna amfani da dabaru daban-daban wajen jan hankali da kuma hulda da masu amfani da kafar yada labaransu domin samun kudi ta hanyoyin gargajiya yadda aka saba da hade da wasu sabbin hanyoyin. Wadannan hanyoyin sun hada da biyan kudi dan sayen labaran, biyan kudi dan zama mambobin shafin, samun kudi ta hanyar karo-karo daga mutane da yawa, fadakarwa kan ayyukan kafar yada labaran, shirya taruka, amfani da kafofin sadarwa na soshiyal mediya, talla da sauransu.

Doriya a wannan fannin abu ne mai wahala ganin yadda yanayin bayanai ke sauyawa a-kai-a-kai. Wannan kundin na GIJN ya duba kalubale, damammaki, da sabbin dabaru daga fannoni da dama, kuma ya dauko ra’ayoyi da nazarin kwararru da da dama.

Shin ko akwai bayanan da ku ke so ku kara a shafin? Ku tuntube me ta adireshinmu na email wato [email protected]

Bangarorinmu sun hada da:

 

Sustainability. Overview/ Dorewa : Gabatarwa

Ana iya karanta bayanai mafi mahimmanci da rahotannin bincike mai zurfi da nazarin halin da fanin aikin jaridar da ba ruwanta da riba ke ciki.

Hanyoyin Tara kudi
Wannan batu ne mai mahimmancin gaske ga kungiyoyi masu zaman kansu. Kundinmu ya yi tanadin bayanai na hanyoyin gano masu bayar da tallafi da yadda ake shiga kawance da su tare da wasu karin bayanai kan hanyoyin tara kudi.

Ma’amala da masu karatu/saurare da hanyoyin samun kudaden shiga
Saduwa da masu karatu/saurare ta yin amfani da sabbin dabaru tare da taimakon soshiyal mediya zai iya habaka yawan masu sauraro da kudaden shiga. Karanta shawarwari daga editocin da ke kan kaba wajen aiki da masu saurare.

Kudin shiga na kasuwanci
Babu shakka samun kudaden shiga na da mahimmancin gaske kuma ana yin wannan wajen amfani da sabbi da tsoffin dabaru. Kwararru a nan suna binciken kalubalen da ake fuskanta wajen samun kudi daga talla, shafukan biyan kudi, biyan kudi dan sayen labaran da ma zama mamba a dandalolin labarai, da hadin gwiwa, da kawancen wallafa labarai, da‘yancin sayar da labarai da sauaransu.

Sauran hanyoyin samun kudaden shiga
Akwai sabbin dabarun da za’a iya amfani da su a madadin wadanda aka saba da amfani da su a baya, wajen tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida. Wadannan sun hada da koyarwa, horaswa, jaridu, rediyo, taruka, hadin gwiwa, kawancen wallafa labarai, biya kadan-kadan, blockchain da Cryptocurrency, sayar da bayanai, zanen shufukan yanar gizo, shirya hotunan bidiyo da sauransu.

Samun tallafi wurin jama’a
Wannan yanzu ya zama ruwan dare wajen gudanar da bincike mai zurfi a aikin jarida. Ko da shi ke, samun tallafin jama’a abu ne da ke bukatar shiri da kuma aiwatarwa yadda ya dace. Ga hanyoyin koyon wannan bisa darussan da aka samo daga wadanda suka taba amfani da shi.

Tasirin bincike
Irin alfanun da aka samu daga bincike mai zurfi a aikin jarida yana da mahimmancin gaske wajen samun goyon bayan masu bayarwa, masu karatu da sauraro da sauransu. Ba abinda za’a yi wada da sho ba ne amma kuma fada ya fi cikawa sauki. Dan haka ku ga yadda ake yi.

 

Sustainability: Perspective – Essential Reading/ Kimantawa – Mahimman abubuwan karantawa

Akwai mahimman rahotanni da suka bayar da ra’ayoyi masu kyaun gaske dangane da sha’awar kirkiro cibiyoyin da za su tallafawa bincike na aikin jarida. Ga mahimmai daga cikin su:

Starting a Nonprofit News Organization, by the Institute for Nonprofit News – Girka tashar watsa labarai mai zaman kanta, wanda cibiyar labarai na kamfanoni masu zaman kansu ta wallafa

Six Strategies for Sustainable Journalism – Matakai shidda na tabbatar da dorewar aikin jarida

DW Academy Media Viability Handbook – Littafin shawarwari dangane da yiwuwar kafuwar tashar yada labarai

Fighting For Survival: New Report on Media Startups in the Global South – Gwagwarmaya don samun tsira: sabon rahoto kan tashoshin yada labarai masu tasowa a yankin kudancin duniya

Publishing for Peanuts: Innovation and the Journalism Start-Up  – Buga labarai ma kudi kalilan: Sabbin dabaru da matakan fara kamfanin aikin jarida

How Nonprofit News Ventures Seek Sustainability: A Knight Study   – Yadda tashoshin yada labarai masu zaman kansu ke neman hanyoyin tabbatar da dorewarsu: Binciken gidauniyar Knight

Financing Quality Journalism  – Tallafawa aikin jarida na kwarai da kudade

Funding the News: Foundations and Nonprofit Media – Tallafawa labarai: Gidauniyoyi da tashoshin yada labarai masu zaman kansu

Venture-backed News Startups and the Field of Journalism  – Kamfanonin labarai masu tasowa da fanin aikin jarida.

A journalism innovation and entrepreneurship reading list  – Jaddawali na abubuwan da za’a iya karantawa dangane da sabbin dabaru na aikin jarida da kasuwanci

The Impact of Charity and Tax Law/Regulation on Not-for-Profit News Organizations – Tasirin sadaka da dokokin haraji kan kungiyoyin labaran da ba ruwansu da riba

Sustainability: A Survival Guide for Nonprofit Investigative Groups  – Dorewa: Jagora ga kungiyoyin masu aiwatar da bincike mai zurfi a aikin jarida

Global Investigative Journalism: Strategies for Support /Hanyoyin tallafawa

The Membership Puzzle na hada gwiwa da kungiyar Luminate da gidauniar dimomiradiyya domin kaddamar shirin mambobi na kafafen yada labarai ta yadda za’a ci moriyar shi har zuwa watan Mayun 2020. Kudin da aka bayar $700,000 zai taimkaa wajen tallafawa mambobin da ke da sabbin dabaru. Domin samun karin bayani kan yadda za’a sami kudin a duba kasa. Babu takamaiman wa’adi. (Spanianci)

Better News /Labarai Mafi Kyau wani shirin ne na Cibiyar ‘Yan jaridan Amirka jo kuma American Press Institute da cibiyar Knight-Lenfest Newsroom Initiative, wanda ke samun kudi daga gidauniyar John S. and James L. Knight wajen shawo kan matsalar dorewar hanyoyin samun kudi.

European Federation of Journalists /Tarayyar ‘Yan Jaridar Turai na nazarin sabbin samfuran kasuwanci wadanda za su taimaka wajen bunkasa aikin jarida.

 

Sustainability: Perspective – More Reading/ Kimantawa – karin abubuwan karantawa

Dalilin da ya sa kafofin yada labarai na yankuna ke fiskantar matsala da hanyoyin sayen labarai a yanar gizo ko kuma digital subscriptions

Tallafawa aikin jarida da kudin gwanati: Birgimar hankaka

‘Yan jarida na fiskantar hadari a kokarinsu na sanya ido kan ayyukan gwamnati, aiki mai mahimmancin gaske wanda ya dace a samar da gidauniya ta duniya na kudi billiyan guda na dalan Amirka

Kungiyoyin labarai masu zaman kansu ba su dogaro da gidauniyoyi, sai dai bayarwa ga aikin jarida na cigaba da karuwa.

Rahotin labaran dijital 2019

Majiyoyi 10 kyauta, na samun bayanai kan masana’antun watsa labarai da masu sauraron labarai

Kalubale 7 da ya kamata a shawo kai kafin a fara kamfani

Cibiyar dorewa ta PBS

Shin aikin jarida mai inganci na iya dorewa? Ga dai kafafin yada labarai 20 da ke shawo kan wannan matsalar.

Kawance, kasancewa mamba da adalci a yanayin zamantakewa: Yadda masu wallafa labarai a yankunan da ke fiskantar danniya ke amfani da sabbin dabaru

Matakai 4 na samun kudaden shiga dan gudanar da aikin jarida

Sabbin dabarun soshiyal mediya 5 da yadda suke tasiri kan masu wallafa labarai.

Aikin jarida na samun tallafi sosai daga masu bayarwa a Afirka: Dalilin da ya sa wannan yanyin ke bukatar sa ido.

Tamboyi 6 da suka shafi shari’a da ya dace duk me niyyar fara kamfanin jarida ya yi la’akari da su.

Makoma biyar na aikin jarida

Wani sabon yanayi ya bulla na yadda manyan jaridu suke sauyawa daga masu kasuwanci da samun riba zuwa masu zaman kansu wadanda ba ruwansu da riba.

Kafafen yada labarai na yanar-gizon da suka zama abin koyi ta fannin albashi a Amirka da Turai: Bayanin 2019

Tinkarar rikicin kafofin yada labarai masu zaman kansu: Irin rawar da taimakon kungiyoyin kasa da kasa zai taka

Ra’ayoyi 50 na samun albashin kafofin yada labarai: Tabbatacen jagora (Kashi na hudu)

Hadin kai a matsayin wani mataki na samun ci-gaba

Shin ko wannan ce dabarar samun kudin da za ta tabbatar da dorewar samun aikin jarida?

Kungiyoyin kula da masu masu saye da sayar da kayayyaki na neman karbar haraji daga kamfanin Facebook domin kare aikin jarida

Yadda za’a fahimci ire-iren salon karatun masu karatu dan jan ra’ayinsu su sayi labarai API

Facebook na kungiyoyi masu zaman kansu – shawarwari 10 da kyawawan misalai Donor Box

“Yanar gizo a kyauta” da farashin shi ga banbancin addini, jinsi, kabila da akida a kafofin yada labarai: Hadarin samar da labarai kyauta CIMA

Shawarwari 11 dangane da sabbin kamfanonin yada labarai Kadan daga cikin rahoton Anya Schifrin na gidauniyar Walkley

Gabatar da INN Index 2018: Halin da labaran kafafe masu zaman kan su ke ciki INN

Wannan ne halis da labaran kafafe masu zaman kansu ke ciki a 2018 Nieman

Hanyoyin samun kudi nawa ne a kafofinn yada labarai? JamLab mun yibayani kan hanyoyi 18

The Publisher’s Patron/Jagoran masu wallafe-wallafe: Yadda shirin labarai na manhajar google ke sauya aikin jarida:

Kamfanin Turai na sanya ido kan ‘yan jarida wato European Journalism Observatory irin kamfanin da ke samun tallafin kudi daga kamfanin google, cibiya ce da gaji kasuwanci a yankin yammacin Turai. A waje guda, kamfanonin labarai masu zaman kanci da wadanda ke aikin gwamnatin ba  u cika samun tallafi ba. Sai dai tambayar ita ce wane buri google ke so ya cimma da wannan tallafin da ya ke bayarwa?

Sabbin dabarun fasahohi na ‘yan jarida karo na 11 (Bidiyo mai tsawon sa’a guda daga Amy Webb)

Rahoton CIMA: Kare kafaden yada labarai masu zaman kance: Cikakken bayani kan yadda kudaden tallafi ke shiga da fita.

Wani bincike ya yi gargadin yadda dakunan labarai a Turai za su fiskanci matsin kaimi a fannonin kudi da na siyasa.

Jagororin Dandaloli: Yadda shafukan Facebook da Google suka zama manyan kamfanoni biyun da ke tallafawa ma’aikatan jarida a duniya.

Sauyin muhallin ‘yan jarida ta yadda ya shafi tattalin arziki.

Karshen bincike a aikin jarida? Tukuna!

Tallafawa ‘yan jaridan da ke zaman kansu shi ne maganin dakile labarai marasa gaskiya wato “fake news” (Yana dauke da rahoton kan tallafawa bincike a aikin jarida)

Rikicin da ake samu a aikin jarida ya zama rikicin dimokiradiyya

Matsalar Cambridge Analytican da ake samu a Facebook zai ce ba’a yi komai ba idan har aka kwaranra da matsalar da za ta afkawa fannin wallafe-wallafe a shafukan yanar gizo.

Tsarin tabbatar da dorewar kananan kafafen yada labarai masu zaman kansu a kan shafukan yanar gizo.

Ceton aikin jarida: Abin da manyan kafafen yada labarai za su iya koyo daga masu zaman kansu.

Shin labaran dijital suna gab da durkushewa ne? Sakamakon binciken cibiyar kamfanin dillancin labarai na Rueters kan kamfanoni bakwai a shekarar 2017

 

Sustainability: Perspective – Case Studies / Dorewa- Misalai

Darussan sauyi daga tsoffin hanyoyin yada labarai zuwa dijital: Shawarwari kadan daga nahiyar Asiya (2021)

Tasirin amfani da sabbin dabaru wajen rubuce-rubuce a yanar gizo: Fitattaun misalai 5

COVID-19 ya ta’azara rikicin dorewar kafafen yada labara a Afirka ta Kudu

Watanni biyu, karin farashi na sa kai da kashi 30 cikin 100 da karuwan masu sayen labarai zuwa 18,000. Abin da eldiario.es suka yi bayan afkuwar annobar COVID-19

Shin sabbin dokokin kamfanonin jarida masu zaman kansu za su taimakawa kamfanonin Canada?

Jagora a kafofin yada labarai na sake wani sabon yunkuri na girka hadakar sabbin dabaru na aikin jarida.

Sakamakon kwarewar da ta ke da shin a shekaru 10, jaridar Texas Tribune na so ta koya muku hanyoyinta na samun kudi

Mun girka wata kungiyar hadin kan kasa dan karfafa aikin jarida mara riba a Jamus

Kungiyar ‘yan jarida ta Outriders ta kaddamar da wani salon da ake kira “pimp my ride” dan taimakawa kafafen yada labarai.

Dabarun da suka yi fice

Mu kaman masu sauraro ne: AJ+ na sake sauya salon labaran shi domin jan ra’ayin matasa.

Yadda kasidu 3 ke amfani da sabbin tsare-tsaren kasuwancin su

Yadda aka samar da Bureau Local

Dabarun dijital na 2019: Misalai daga manyan jaridu biyar (5)

Yankin Kudancin Asiya: Tallafawa aikin jarda a zamanin dijital

A jihar Texas, ‘yan jarida masu zaman kansu na yunkurin cike gibin da masu kafofin yada labarai na kudi ke bari.

Sauya kamfanonin jaridan (Canada) zuwa kungiyoyin tallafi: Sabon salon nan gaba?

An sake yin saki na dafa: Kafofin yada labarai a yanar gizo za su iya tsira?

Jarida La Presse ta Montreal za ta daina karbar kudi.

Aikin jarida mara riba a duk fadin duniya (Cikin Jamusanci)

 

Fundraising/ Tara Kudi

Fund raising: Essential reading /Tara kudi: Mahimman Abubuwan da suka dace a karanta

Tara kudi dan farawa ko inganta kafafen bincike na aikin jarida masu zaman kansu na da kalubale. Tallafi da kyautan da ake samu daga kungiyoyi da mutanen da ke bayar da tallafi kafa daya ce kadau. Ga wasu shawarwari daga wadanda suka shahara wajen tara kudi:

SABO: MediaDev shawarwari na tara kudi (2021)

Shawarwari: Bincike da bayanai kan tara kudi, daga gabatarwar Bridget Gallagher a GIJC19

Masu bayar da agaji: Wa ke tallafawa me

Masu tallafin da ke tasiri a kafafen yada labarai

Tallafin labaran kasa da kasa: fitar da taswirar hanya

Hangen nesa da girbi: Yadda ake share-fagen tara kudi

Hangen nesa: Mahimman bayanai

Yadda ake rubuta farfosa ta samun kudi – Shawarwari da darussa

Bayanai kan masu bayar da agaji

Hanyoyin samun kudin tallafawa ma’aikatan jarida masu zaman kansu

Hanyoyi bakwai na yadda kananan masana’antu da masu matsakaicin karfi ke rage wa kansu karfin tara kudi

Sirrin tara kudi: Babban aiki mai bukatar karfin hali

Zana taswirar hanya a fannonin da suka shafi tara kudi

Hanyoyi 8 na inganta hanyoyin samun kudi ta yin amfani da “Gift ladders” – tsarin da ya kunsho karbar kyauta daga dan kankani zuwa mai yawan gaske.

Shawarwari daga babban tarin GIJC na 2013

Bidiyo

 

Fund Raising: More Reading /Tara Kudi: Karin abubuwan karantawa

Masu tallafawa kafafen yada labarai a Jamus na karuwa

Idan aka yi tayin kudi, mu kan saurara: Yadda dakunan labarai 8 asu zaman kansu suka yi nasarar kara yawan tallafin da suke samu

Masu bayar da kudin aikin jarida: Kasida ce mai fitowa wata-wata, da bayanai kan wadanda ke jagorantar sauyin da ake yi a fagen bayar da tallafi da aikin jarida a Turai.

Mutane 50,000 masu bayar da tallafi a karon farko? Ga yadda wadansu kafafen yada labarai hudu, masu zaman kansu suka ci moriyar NewsMatch

Kudaden tallafi na matukar bukatar karuwa

Samun tallafi daga gidauniyoyi da matsalar iyakokin da ake da su a aikin jarida

A nan akwai taskar da ke kunshe da ababen taya hasashe, bincike da rubuta rahotanni na cibiyar Future Today

Yadda za’a kaucewa labarai na sa’o’i 24n da ke cikin yini bakwai – Cibiyar kafafen yada labarai, bayanai da al’umma. Hira da babban darektan gidauniyar Fritt Ord da ke Kasar Norway.

Hanyoyin karbar kudi a manhajan Facebook sun fara karbar biya na wata-wata

Hanyoyin tara kudi a Facebook FTW

“Fitattu masu mara ma fitattu baya.” Mene ne laifi (ko daidai) wajen girka gidauniyoyin da za su tallafawa aikin jarida

Labaran tallafi: Gidauniyoyi da kafafen yada labaran da ba ruwansu da riba

Hanyoyin samun kudi masu aiki

Hanyoyi biyar na yadda masu zaman kansu za su iya burge masu bayar da tallafi ta yin amfani da tallan imel.

Shawarwari dangane da hanyoin tallafawa aikin jarida da kafafen labarai dan wadanda ke sha’awar shiga wannan fannin.

Aikin jarida da samar da tallafi ga kafafen yada labarai: Batutuwa biyar da ya kamata ku sani da hanyoyi biyar na farawa

Shawara: Yanzu ana iya tsara dangantakar nan gaba tsakanin ‘yan jarida da masu bayar da tallafi

Sirrin kulla kyakyawar dangantaka tsakanin ‘ya jarida da masu bayar da tallafi.

Rike masu bayar da tallafi ya fi samun sabbi sauki

Kungiyoyin agaji da dakunan labarai masu zaman kansu a yankin kudancin duniya (wato Afirka)

Ba kullun ne bakin masu bayar da tallafi da dakunan labaran da suke tallafawa kan zo day aba “Banbanci tsakanin sanya baki tare da amincewar wadanda abin ya shafa da kutse.”

Tambayoyi hudu da dakunan labarai wadanda ba ruwansu da riba da masu bayar da tallafi ke da su kan dangantakarsu da ke sauyawa kullun.

Wadanne irin kalubale da damammaki ake samu wajen tallafawa aikin jarida a Birtaniya?

Shawarwari hudu (4) ga ‘yan jaridan da ke neman tallafi daga gidauniyoyi.

Attajirai ko kuma masu mallakan billiyoyin kudade ba za su iya gyara tsarin kasuwancin aikin jarida ba

Nasarorin matakan da dakunan labaran California masu zaman kansu suka samu da masu tallafa musu da kudade.

Shawarwari dangane da hanyoyin samun kudi daga Mother Jones

Gidauniyoyi da ginshikin sabon hanyan samun kudi dan gudanar da aikin jarida

Abubuwa biyar da ya kamata a yi cikin wuni daya bayan kammala taron neman tallafi

Damammaki da iyakokin da ake gamuwa da su wajen aikin jaridar da ke samun tallafi

Bincike da girbi: Hanyoyin gudanar da shirye-shiryen neman tallafi (Bridget Gallagher 2014)

Shawarwari dangane da hanyoyin samun kudi daga babban taron GIJN 2013

 

Audience Engagement and Revenue: Essential Reading / Jan hankalin masu sauraro da samun kudaden shiga: Mahimman karatu

A ko’ina dakunan watsa labarai na la’akari da mahimmancin samun hadin kai ko kuma ma’amala da masu sauraonsu da ma yadda gudanar da abubuwa a fili da samun hadin kan jama’a ke haifar da dangantaka mai aminci wanda kuma zai iya kawo kudaden shiga. Akwai samfura da dama na samun kudade, kuma kungiyoyi masu zaman kansu wadanda ke gudanar da bincike mai zurfi a aikin jarida na gwagwada wadannan samfuran domin su gano wadda za ta fi dacewa.

Reader Revenue Toolkit/ Dabarun samun kudi daga masu sauraro/karati

14 steps to use collaborations ro create better journalism and boost revenue/ Matakai 14 na amfani da hadin gwiwa dan inganta aikin jarida da kuma habaka kudaden shiga

More than meet the Eyeballs: How Journalism can benefit from Audience Engagement/ Yadda ma’amala da masu sauraro ko karatu zai inganta aikin jarida

Lessons on solving the Media Membership Puzzle/ Darussa na hanyoyin shawo kan matsalar jan hankalin masu sauraro su rungumi matakin kasancewa mambobi a kafafen yada labarai

Guide to audience Revenue and Engagement/ shawarwarin hulda da masu saurao/karatu da samun kudaden shiga

Reinventing the Rolodex: Why you should ask your members what they know/ Sauyi daga abin da aka saba: Abin da ya sa samun shawara daga masu sauraro ke da mahimmanci

Paths to Subscription: Why Recent Subscribers choose to pay for news/ Hanyoyin samun masu biyan kudi ma labarai wata: Dalilan da ya sa wadansu masu sauraro/karatu ke biyan kudi wata-wata dan samun labaran.

Engagement or Reach: How to best find our Audience – Ma’amala da masu sauraro ko daukan matakan samun dogon zango dan kara yawan masu sauraro: Hanyar da ta fi tasiri wajen samun masu sauraro da suka fi dacewa da mu.

 

Audience Engagement and Revenue: More Reading / Jan hankalin masu sauraro da samun kudaden shiga: karin karatu

Darussa hudu daga editocin zamani na Instagram da dakunan labaran cikin guda

Yadda bayanai za su taimakawa dakunan labarai wajen yanke shawara kan mambobinsu

Hanyoyi 231 da mawallafa za su iya samun kudi

Mawallafa 3 cikin 4 sun fitar da sabobin hanyoyin cimma bukatun da suka bulla da zuwan COVID-19, “Daga sauya suffer kamfanin zuwa sabbin hanyoyin samun kudaden shiga”

“111% more article clicks”: Yadda wata sabuwar alama a shafin Facebook zai iya taimakawa mawallafa wajen yin ma’amala da masu karanta rahotanninsu

“Labarai na sauyawa a hanyoyi masu kayatarwa”: Yadda mawallafa ke amfani da manhajan Instagram su ja hankalin matasa su kuma kara yawan masu sauraro/karanta labaran su

What if Scale Breaks Communitya: Hanyoyin cigaba da ma’amala da al’umma sadda aikin jarida ke fuskantar kalubale

Binciken da aka yi kan manyan kamfanonin yada labarai 600 ya bayyana mahimman dabaru hudu da mawallafa za su iya amfani da su wajen inganta ma’amalarsu da masu sauraro.

Shawarwari ga kamfanonin da ke neman ma’amala da mambobinsu da kuma habaka kudaden shiga

Da ruwan ciki ake jan na rijiya Hanyoyin zuba jari wadanda ta su habaka yawan mambobi

Abin da za mu iya koyo daga komawa matakin samun mambobi

Pico na neman sanya fasahar CRM a shafukan kafofin yada labaran da ke hankoron samar da dangantaka tsakaninsu da masu sauraronsu – Nieman Labs

Shwarwari biyar (Da misalai da dama) na yadda za’a iya ma’amala da amsu sauraro a dakunan labaran Turai

Daukar jagorancin sha’awar da ke karfafa samfurin sayar da labarai ga mambobi WAN-IFRA

Dakunan labarai sun fara mayar da fifiko kan wadanda suke nuna musu aminci fiye da yawan lokutan da aka karanta labaran da suka wallafa. Poynter

Bayanai kan abin da ya sa masu sauraro ke yarda su biya dan labarai. Twipe

A goge labaran da babu wanda ya karanta. A gabatar da abubuwa na bazata da sauran dabaru na jan hankalin masu sauraro Niemand Lab

Darussa biyar daga dabarar samun mambobi na jaridar Guardian, na tsawon shekaru 3 yanzu a Journalism.co.uk

Kowa na cewa samun mambobi shi ne makomar aikin jarida. Ga yadda za ku iya aiwatar da wannan Rob Wijnberg wanda ya kirkiro de Corespondent

Barkan ku da zuwa shawarwarin samun kudaden shiga daga masu sauraro/karatu Cibiyar ‘yan jaridar Amirka

Ma’amala da masu sauraro zai iya kasancewa mafi mahimmanci ga dakunan labarai: Darussa 4 da ya kamata a duba RJI Online

Akwai bukatar habaka masu sauraro ko karanta ayyukan ku? Ku kawo editan habaka Atlantic 57

Tantance batun samun mambobi: Abin da ya sa kasancewa mamba da biya wata-wata suka kasance abubuwa daban-daban

Ba kwa sauraro yadda ya kamata: yadda ‘yan jarida za su iya magana kadan, sauraro da yawa domin taimakawa al’ummomi yadda ya kamata

Abin da ya sa masu labarai ke neman mambobi duk da cewa kudin kalilan ne

Mun tattauna da daruruwan mutane masu zaman kansu wadana ke tallafawa labarai a bara. Ga abubuwan da suka bayyana mana

Shawararmu dangane da aikin jaridar da masu sauraro za su dauki nauyi nan gaba da yadda za ku iya karawa da naku

Idan ya zo ga kaddamar da shirin mambobi da gaske kuma mai dorewa a aikin jarida, ku bukaci da yawa.

Idan har kamfanonin labarai suka rungumi tsarin ma’amala da masu sauraro, kudin zai biyo baya?

Hanyoyin samun kudi ta yin ma’amala da masu sauraro

Abin da shafinku zai iya koyo daga shafukan labarai 100 da ke da kwararan shirye-shirye na mambobi

Abin da wata kafar yada labaran da ta durkushe za ta iya koya mana kan damawa da masu sauraro wajen samar da rahotanni

Lokaci ya yin a gudanar da hadaka mai amfani

Shin “Engagement” ko kuma hulda babbar kalma ce kawai?

Neman shawara daga wajen masu sauraro/karatu

Lokacin da tsarin mambobi bai dace ba

Masu karatu yawanci sun fi so biya kudi dan samun labarai dangane da wani gari ko wuri – Shafukan da aka gina kan wadansu mahimman batutuwa fa?

Rahoto: “Hanyoyin hulda; Fahimtar yadd dakunan labarai ke aiki da al’ummomi”

Tsarin mambobi na kasancewa alfanu ga wadansu kafofin labarai

Tsarin aikin da ya fi dacewa ma dakunan labarai su yi amfani da shi wajen biyan bukatun al’ummomin da suka shahara a abubuwa na musamman.

Watakila muna da halin kirki, tunda mun yi imanin cewa samun tallafin kudi daga masu sauraro/karatu ne kadai zai sa mu cigaba da kasancewa masu ‘yancin kan mu.

Wat hira da farfesan NYU kuma mai sharhi kan abubuwan da suka shafi kafafen yada labarai Jay Rosen kan dalilin da ya sa samun mambobi zai kasance hanyar tabbatar da dorewar aikin jarida a matsayin hanya ta yi wa kasa hidima.

Wannan shirin rahotannin na neman samun damar gudanar da bincike mai zurfi kan lamuran da suka shafi muhalli ma mutanen da ke bukata.

Sabbin dabari a aikin jarida ta hanyar amfani da tsarin hulda da jama’a

“Hello da mutun a wurin?” Auna hulda da masu sauraro da rawar da suke takawa.

 

Audience Engagement and Revenue: Case Studies / Jan hankalin masu sauraro da samun kudaden shiga: Misalai

Memberkit 101: Inganta nazari da kuma gina kundin bayanai na samar da tsarin mambobi

Karfin amfani da sabbin dabaru wajen aiwatar da aikin jarida na gargajiya a shafukan yanar gizo: Kwararan misalai biyar

Binciken masu karatu/sauraro a jaridar The Atlantic: Yadda mu ke amfani da shi- da abin da muke tunanin ba zai yi mana ba

“ThinkIn” outside the box: Yadda mawallafa ke amfani da tattaunawa na musamman da sukan yi da mambobinsu wajen inganta ayyukansu da kuma samun labarai

Gudanar da aune-aune domin cimma burinmu: Auna tasirin City Bureau

Ana iya tura labarai a matsayin sakon text? Sabuwar jaridar The New Paper a Indiana na tunanin haka.

Da mambobi 7,000 rayuwarmu ya riga ya sauya”: Yadda jaridar The Daily Maverick ta kirkiro shirin mambobinta

Darussa da labarai daga shekaru 130 na kasancewa mamba a kasidar National Geographic. Membership Puzzle

Ku shiga Kulob: yadda bukukuwa irin su Burning Man da sauran kungiyoyin hadin gwiwa ke taimakawa aikin jarida. Hadin gwiwar kafafen yada labarai ne samfurin kasuwancin nan gaba?

Hadin gambiza, gungun shafukan labarai a yankin Asiya sun rungumi wani salon a bunkasa a hankali da fahimatar masu sauraro/karatu

Wasu ‘yan jarida, Amirkawa masu asalin Iberiya sun samar da wata sabuwar dabara na samar da bayanai ta yin amfani da sabbin fasahohi da kirkiro al’umma

Tsarin kowa ya biya kudin iya abin da ya saya: De Correspondent zai je Amirka da sabon salon sayen bayanai.

Abubuwa 4 da HBR ya koya bayan aiwatar da gwaje-gwaje da masu sauraro

Yadda wata kafar yada labarai na cikin gida Berkeleyside ya tara dala milliyan guda ta karbar kudi kai tsaye daga al’umma

Aiki da mambobi, jaridar Republik na neman nuna cewa akwai bukatar labarai irin wanda masu sauraro za su biya su samu a Switzerland

Ta hanyar tura sakonnin text zuwa mazauna yankunan cikin gida, Outlier Media na hada masu neman labarai wadanda ke da masu karamin albashi da bayanai masu amfani irin wadanda su ke bukata.

Yadda tashar VOX ke amfani da kungiyoyin shafin Facebook ya gina al’umma

PolitiFact ya tara $105, 000 cikin kwanaki 20 da sabon shirin shi na rajistan mambobi

Gather zai samar da dandalin da zai gano amsoshin tamnayoyin da ke kewaye da tsarin ma’amala da masu sauraro.

Sabon dandalin Gather na da burin hada ‘yan jarida da tallafa wa wadanda ke aiki wajen hulda da jama’a.

Yadda De Correspndent he horas da marubuta dangane da ma’amala da masu karatu da kuma shiga Tsakani a matsayin jagoran tattaunawa ko kuma “discussion leader”

Misalan huldodin ‘yan jarida masu zaman kansu da masu sauraro/Karatu ( A Amirka)

Abin da mambobi ke cewa dangane da dalilan da ya sa suke goyon bayan De Correspondent

Cikin sa’o’i kalilan shirin The Marshalll ya sami makudan kudi daga sabon shirin shi na rajistan mambobi

Jaridar The Atlantic ta kaddamar da wani shirin da ya bukaci mambobi su biya mai suna The Masthead

Yadda Mother Jones ke yin aikin jarida a zamanin hotunan bidiyon maguna: Suna tambayar kudi

Sabuwar kamfanin Dutch The Playwall ba baiwa masu karantawa zabin biya ta yanar gizo bayan sun amsa wasu tambayoyi

Yadda wannan jaridar ke jan hankalin mambobinta: Damawa da su tun a lokacin hada labaran.

Guardian ta gudanar da bincike kan dakunan labarai masu hulda da mambobi kawai a duk fadin duniya

De Correspondent yanzu yana da mambabi dubu 50 masu biya: Kalubale uku mafi girma a shekarar 2017

Hanyar kaiwa milliyan guda: Jaridar The Gurardian tashi daga mambobi dubu 15 masu biya zuwa dubu 200 a bara kawai

Tsarin wata al’umma ta gudanar da bincike mai zurfi a Canada ya sami karbuwa a matakin kasa baki daya

 

Audience Engagement and Revenue: Newsletters / Jan hankalin masu sauraro da samun kudaden shiga: Wasikun labarai

Domin jan hankalin masu karatu bayan COVID-19 mawallafana ganin cewa rubuta wasikun da ke dauke da labarai da kuma shirye-shiryen rediyo na podcast za su fi tasiri

Yadda kamfanin Indiegraaf ya kaddamar da tashoshin labaran cikin gida guda 6 lokacin COVID-19

Wasikun labarai na da mahimmanci wajen tabbatar da amincin masu karantawa. Ga yadda za’a iya cin moriyar su

Ba wasikun labarai ba, jagora na wata-wata

Bayani kan dabarun tsara wasikun labarai

Yadda sabbin dabarun samar da wasikun labarai ke baiwa mawallafa kudaden shiga. Mene ne sabo a duniyar Wallafa

Shawarwari 201 na inganta wasikun labarai – habaka yawan masu samu, karin kudi da sauransu. Newsletter Guide

Hanyar inganta wasikun labarai Betternews

Yadda masu wallafa wasikun labarai za su iya maido kwastamominsu Digiday

Kai wasikun labaran imel zuwa kashi 78 Digital Content Next

Dabarun hulda da jama’a domin bunkasa yawan al’umma da masu karantawa Medium

Yadda za ku iya fara na ku wasikun labaran

Darussa 6 kan imel da bunkasa yawan masu sauraro/karantawa a labaran kamfanonin da ba ruwansu da riba

Abin da nazarin wasikun labaran Axion 1,300 ya koya mana

Yadda jaridar Wall Street ke kwaskware wasikun labaranta – tana kuma kokarin kara alkinta ta.

Wasikun labarai mafi kyau

Abin da ya sa jaridar New York Times ke son wasikun labarai gajeru

Ga duk abubuwan da ya kamata ku sani dangane da wasikun labaran da ake biya, wasikun labarai na gajeren lokaci, gajerun labaran safe da kuma wasikun labaran al’ummomi

Farillan rubuta wasikun labarai: Rubuta imel

Amfani da kayan aikin kimiyyar bayanai wajen nazarin masu karanta imel

Jaridar Politico mallakar Brazil? Mai samun tallafi daga wasikun labaran da ake biya Poder360 na gudanar da bincike kan madafun ikon kasar.

Darussan da aka koya daga bunkasar wasikun labaran Vox Media

Gina wasikin labarai mai inganci

Yadda ya dace a rubuta sakon imel mai dauke da wasikun labaran da masu karantawa za su karanta da gaske

Hanyoyi hudu da wasikun labarai za su iya kaiwa akalla kashi 50 zuwa 60 cikin 100

Ka shawarwari 42 na rubuta wasikar labaran dakunan watsa labaranku na nan gaba.

Abu daya da kowace kafar labarai na dijital ke bukata ita ce Wasikun labarai,

Amfani da kayayyakin aikin kimiyyar bayanai don nazarin masu karantawa: Jagorar bincike

Kuna so ku fawa wasikar labarai? Ku fara da karanta wannan NPR guidance on design 2016

 

Audience Engagement and Revenue: Events / Jan hankalin masu sauraro da samun kudaden shiga: Taruka

Salon shirya taruka masu mahimmanci na hulda da jama’a Todd Milbourn and Lisa Heyamoto

Shawarwari na shirya taro kai tsaye mai marawa aikin jarida baya

Yadda ake kaddamar da sana’ar shirya taron da zai yi nasara

Yadda ake amfani da kafofin yada labaran al’umma wajen shirye taruka kan tatsuniyoyi da labaran da za su ja hankalin masu bayar da kudin tallafi kyauta

Jaridar The New York Times tana kara inganta shirinta na kiran masu sayen labaranta kai tsaye su yi hira kamar yadda ake yi a rediyo

Yadda wata jarida ta kaddamar da wani shirin wakokin adabi na rap domin ta inganta talla

Aikin jarida kai tsaye: Yadda shirye-shirye ke tabbatar da huldodi da kuma bunkasa yawan kudaden shiga

Wata jaridar da ba ruwanta da riba a New York ta tara dalan Amirla $7100 da makida da tallan hotunan zanen da garaya.

 

Commercial Revenue/ Kudadne shiga daga hada-hadar kasuwanni

Commercial Revenue: Essential Reading/Kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanni: mahimman batutuwan karantawa

Kudaden shiga na kasuwanci na daukar suffofi daban-daban kuma zai iya bayar da karin kudin da ake bukata a kungiyoyin yada labaran da ba ruwansu da riba ko kuma ma cikakken tallafin da su ke bukata. Wannan ya hada da talla, da kudaden da masu sayen labarai ke biya wata-wata da sauransu:

Labaran Google da INN sun wallafa littafi mai tsokaci kan yadda kafofin labaran da ba ruwansu da riba za su iya samun kudaden shiga- Littafi ne da ke nuna wa dakunan labarai yadda za su bunkasa kudaden shiga daga talla, masu daukan nauyin taro, karban kudi dan wallafa wadansu batutuwa da ma sauran hanyoyin samun kudi.

Yadda ya kamata a auna kudaden shiga na kasuwanci a matsayin dabara ta tabbatar da dorewar kafafen yada labaran da ke bincike mai zurfi. A wannan kasidar, mawallafi Ross Settles ya mayar da hankalu ne kan kafofin yada labarai na dijital da kasuwanci a cibiyar aikin jarida da nazarin kafofin yada labarai da ke jami’ar Hong Kong

Darussa na koyarwa da koyon aikin jarida na kasuwanci da (Duba kwatancen da Jeremy Kaplan, darectan illimi a cibiyar Tow-Knight na aikin jarida na kasuwanci a jami’ar birnin New York)

Sabbin hanyoyin da mawallafa za su iya samun kudaden shiga daga yanar gizo

Reader Revenue Kit – Taska mai kunshe da labarai kan batutuwa daban-daban wadanda ke hannun American Press Institute

Commercial Revenue: More Reading/ Samun kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanci: Karin Karatu

Dalilin da ya say a kamata a raba aikin jarida daga kudaden tallafin da ke zuwa daga hada-hadar kasuwanni

Rikicin kamfanin Fortnite da kamfanonin Apple da Google zai iya yin tasiri kan kamfanonin da ke buga jaridu da litattafai

Shawarwari masu amfani wa kungiyoyin masu yada labarai dangane da hanyoyin tantance dabarun samun kudi

Yadda jaridar Washington Post ke daidaita tsakanin kudaden da take samu daga talla da wadanda ke zuwa daga kudin da ma

su karanta labaran ke biya wata-wata- Digiday

Dabarun da ake amfani da su wajen sauya kafar yada labarai zuwa wadda za ta rika samun kudi daga masu karanta labaran. Cibiyar ‘yan jaridan Amirka. ‘Yar gajeruwar jagora kan kalubale na fasaha da dabarun da akan fiskanta wajen samar da tsarin karbar kudi

Alfanu da rashin alfanun babban jarin kafar yada labarai daga kasidar Columbia Journalism Review

Kamfanin Apple na magana da manyan kamfanonin jarida dangane da yiwuwar hada gwiwa da su a shirin ssu na biya wata-wata. Recode

Sabbin hanyoyin da mawallafa za su iya samun kudi daga yanar gizo

Hanyar kaddamar da kwas mai riba sosai a yanar gizo yayin da ake bunkasa yawan masu sauraro

Kalaman batsan da ‘yan jarida za su iya amfani da su, ba tare da jin kunya ba

Sabbin fasahohi da ke share fagen gudanar da aikin jarida mai riba

“No silver bullet”: Duk da irin karuwar da mawallafa ke samu a kudaden shiga, bai kai yawan kudin da suke rasawa a talla ba

Mutane na biyan kudi dan samun bayanai: Ga yadda mawallafa ke cin moriya.

Mahaukaciyar shawara na samun kudin tallafawa labaran cikin gida: A sa jama’a su biya

Yayin da kungiyoin yada labarai a duniya ke cigaba da fama da karancin talla, da yawa sun fara mayar da hankali kan daidaikun da ke sayen labaran daga wurinsu.

Sabbin kamfanonin labaran da ke da jari da fagen aikin jarida

Damammakin sabbin kamfanonin yada labarai a kamfaninin labarai

Dangataka mai sarkakiyar da ke tsakanin kafofin yada labarai da tallafin VC

Sabbin kafofin yada labarai: ‘yan jarida kan sauya su zama ‘yan kasuwa ne dan tabbatar da aikin jarida mai inganci

Yadda Buzzfeed ke gina hanyoyi daban-daban na samun kudi ba tare da taimakon Facebook ba

Jeff Bezos na da shawara ga masu kamfaninin yada labarai: “Ku ce mutane su biya. Za su biya”

Wanda ya yarda da labarai kuma yana biya dan samu

Martin Baron: “Akwai kasuwanci hade Imani a batun gudanar da bincike mai zurfi a aikin jarida

Commercial Revenue: Advertising/ Samun kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanci: Talla

Tsarin tallar da ya lilace ya kan baiwa masu aikata miyagun ayyuka damar satan bayanai cikin sauki

Tallace-tallace na dijital a Amirka ya wuce billiyan 100 na dalar Amirka a shekarar 2018 – Tech Crunch

Binciken hanyoyin samun kudi a yanar gizo Mozilla

Shawarwari kan fasahar talla Tow Center

‘Yan jarida na shakkun fasahohin talla amma kuma sun dogara da shi. CJR

Mene ne sabo a duniyar wallafa litattafa, bayanai 50 na sanya kafafen yada labarai biya. (Kashi na biyu)

An fara daina kasha kudi kan talla a Amirka, yayin da masu wallafa kasidu ke cigaba da fiskantar matsala WWD

Jaridar Financial Times ta kirkiro wata fasaha ta nazarin masu sauraro/ karantawa domin bunkasa talla da maimaita wadanda suka sami karbuwa Digiday

Karshen talla na gargajiya kamar yadda kuma san ta. Rahotn Nieman

Commercial Revenue: Subscription/Paywall/ Samun kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanci: Biyan kudi

Hanyoyi 7 da COVID ya yi tasiri kan dabarun da ake amfani da su wajen biyan kudi don labarai

Yadda ake kirkiro tsarin da ya tanadi masu karanta/sauraron labarai su biya: Darussa daga kasashen Spainda Burtaniya

Samun mambobi a kafafen yada labarai zai taimakawa aikin jarida kuma zai taimaka mi shi ya yi sauyi: Me ya sa mawallafa suke neman bunkasa fiye da masu biyan kudi dan labarai

Watakila tsarin biyan kudi ba zai yi muku aiki ba

Yadda kasidar Economist ta ninka yawan mutanen da ke biya sau uku ta yin amfani da manhajan LinkedIn

Yadda mawallafan yau za su iya amfani da bayanai, da misalan ayyukan da szja yi ficce su kuma koyi dabarun gina sabbin hanyoyin samun kudi

Tabbatar da tsaro a wurin biya! (Da wasu darusssa daga binciken da aka yi a kamfanoni 500 na masu wallafa jaridu

Yadda dakunan labarai za su yi kara yawan masu sayen labarai wurinsu da ma’amala da su Lens Fest

Chartbeat ya shafe sa’o’i 400 yana nazarin hanyar sayen labarai na subscription – Ga abin da muka gano. Digital Content Next

Zuba jari a hanyar biyan kudi na subscripzion zai kawo bunkasa na kashi 2000 cikin 100 – International New Media Association

Commercial Revenue: Subscription/Paywalls – Case Studies/ Samun kudaden shiga daga hada-hadar kasuwanci: Hanyoyin biyan kudi – Misalai

Commercial Revenue: Syndication, Publishing Partnerships, Rights Sales/ Hadin gwiwa, kawancen wallafa, ‘yancin sayarwa

 

Crowdfunding/Samun gudunmawa daga jama’a

Crowdfunding: Essential Reading/ Samun gudunmawa daga jama’a: Mahimman karatu

Binciken GIJN na bayar da shawarwari dangane da ya kamata a tsara a kuma aiwatar da gangamin neman kudi daga jama’a, sunayen shafukan kasa da na yankuna da ake aiwatar da irin wannan gangamin da ma irin dabaru da abubuwan da ya kamata a yi amfani da su.

A babban tarn GIJN wanda aka gudane a birnin Hamburg Tamas Bodoky na Atlastszo da ke kasar Hungary, ya fadada wannan a karkashin rukunoni bakwai (kuna iya ganin cikakken bayani a nan tipsheet)

  1. Samar da hanyoyi da dandaloli daban-daban na karbar gudunmawa
  2. Mayar da hankali wajen samun gudunmawa da yawa daga wadanda za su rika bayar da kadan amma a kai-a kai.
  3. A kasashen da karkashin mulkin da ba shi da sassauci, masu bayar da gudunmawa sun fi so a sakaya sunayensu
  4. Kayayyakin kyauta ko saidawa masu dauke da tambarin kamfanin/kafar yada labaran suna taimakawa wajen samun masu bayar da gudunmawa
  5. Talla na da mahimmancin gaske
  6. A yi amfani da abubuwa masu kayatarwa da ban dariya wajen shirya gangamin karbar gudunmawar daga jama’a
  7. Auna abin da ke aiki da wanda ba ya yi

Domin karin bayani duba shafin GIJN

  • Samun gudunmawar jama’a domin ‘yan jarida
  • Shawarwari dangane da samun gudunmawa daga jama’a
  • Shafukan samun tallafin jama’a a duniya baki daya
  • Shafukan yankuna
  • Shawarwari da darussa
  • Ababen shirya gangamin samun gudunmawa daga jama’a na kyauta

Abubuwan da ya dace ku yi kafin ku fara neman tallafi daga jama’a Cibiyar ‘yan Jaridan Turai

Mun yi nasarar shirya irin wadannan gangamin: Ga wasu darussan da muka dauka. Kuna iya amfani da su wa dakunan labaranku

 

Crowdfunding: Case Studies/Samun gudunmawa daga jama’a: Misalai

Yadda kafar yada labaran the correspondent ta tara milliyan biyu da rabi na dala ($2.5m) cikin kwanaki 29 Engaged Journalism

Kafar tara wa ‘yan jarida gudunmawa daga jama’a ta sami lambar yabo na kasancewa gwarzo a masana’antan fasaha da kafafen yada labarai a kasidar kasuwanci na kasar New Zealand mai suna New Zealand Herald

Kafar da ke amfani da tallafin jama’a wajen gudanar da aikin jarida inda ma’aikatan jarida bas u da ‘yancin walwala sosai. Kasidar da ke bitar ayyukan jarida a Columbia

Bayan da ta yi nasarar samun gudunmawar jama’a kasidar Ssiss Republik ta fara tsara sabuwar taswirar hanyar “mayar da aikin jarida bisa turbar da aka fi sani” Nieman Lab

A Italia, Il Giornale na amfani da tallafin jama’a ne wajen kawo rahotanni daga yankunan da ake yaki

Jaridar The Guardian a Amirka ta sami sama da $50,000 dan yin rahotanni dangane da filayen jama’ar da ake saidawa

OCCRP Crowd Funding Campaing

 

Special Topics/Batutuwa na musamman

Special Topics /Batutuwa na musamman: Podcasting/ shirye-shiryen saurare

Wasu hanyoyin samun kudaden shiga: Podcasts/ shirye-shiryen saurare kan yanar gizo

Hanyoyi 8 da mawallafa za su iya samun kudi da shirye-shiryen Podcast

Jagoran mawallafi kan podcast: Sauke rahoton

Samun tallafi dan shirye-shiryen rediyo da na saurare kan yanar gizo

Makomar shirye-shiryen podcast it ace zamar da sun a biya – Darussa daga tarihin kafofin yada labarai

Da manyan taurari a fanin fina-finai da nishadi da kuma kudaden biya Luminary na kokarin zama Netflix na shirye-shriyen podcast.

Abin da ya sa rediyo zai yi dadin sana’a

Mutane millyan 10 suka sauke shirin podcast din da ya yi bincike dangane da batun cewa malaman makaranta sukan sami dalibi daya da suka fi so cikin duka dallabansu, abin da aka fi sani da teacher’s pet a turance

Dalilai 7 da ya say a kamata ku saurari shirye-shiryen podcat

Samun kudi daga shirye-shiryen podcast.

Special Topics /Batutuwa na musamman: Micropayments/Biya kadan-kadan

Abin da ya sa tsarin biyan kudi kadan-kadan bai mutu ba

Hanyoyin jan hankalin masu karanta labaran da aka sanya a yanar gizo har su so biyan kudi – daga biya kadan har ziwa biyan kudade a soshiyal mediya. Kawancen Editocin Duniya. (Global Editors Network)

A Winnipeg na kasar Canada biyan kudi kadan ba ya wani kawo makudan kudi amma kuma dabara ce mai kyau wajen samun abin da ake bukata

Kamar yadda ake sauya yanayi mawallafa sun sake komawa ga karbar biya kadan-kadan

Special Topics /Batutuwa na musamman: Blockchain and Cryptocurrency/ sabbin fasahohin kudi

Links on other sites and other languages

Special Topics/ Batutuwa na musamman: News Co-operatives/Kungiyoyin labarai na dafa wa juna

Sabin tsarin kasuwanci ya bulla:  Ga labaran dijital na hadin gwiwa

Tsokacin Edita: An fara wallafa wannan labarin ne a jaridar Non-Profit Quaterly (NPQ)- Jaridar da ke fita bayan kowani watanni uku a yanar gizo ranar 3 ga watan Maris 2021. Muna farin cikin sake wallafa mu ku shi a nan da izinin su. Duk da cewa labarin ya fi mayar da hankali kan kasuwannin Amirka ne akwai darussan da duniya za ta iya yin koyi da su. Hakika, kamar yadda labarin ya bayyana, dadaddu jaridun hadin gwiwar da masu karantawa ne ke jagora na na a kasashen Turai, da Mexico kuma sun fara samun tushe a kasashen Canada da Uruguay

Cikakken yunkurin jama’a ke nan: Rabon da dimokiraddiyarmu ta yi rauni haka tun lokacin yakin basasa, a yanzu ba wanda ya yadda da cibiyoyin gwamnati, kuma kafar samun labaran cikin gida mai cike da tarihi wanda ke karfafa jama’a – wato jaridun al’ummomi – suna ta fuskantar koma baya na tsawon shekaru fiye da goma. Kashi daya cikin hudu na jaridun Amirka sun rufe tun shekarar 2004 kuma annobar COVID-19 ta sake ta’azara wannan matsala.

Bacin yunkurin da ake yi na fadada matsalar mutuwar kamfanonin jaridun da sabbin shafukan dijital – wasu masu burin samun riba wasu kuma ba ruwansu da samun riba – adadinsu ba ya karuwa da sauri kamar yadda ake so, dan sum aye gurbin wadanda ke bata. Binciken jami’ar jihar North Carolina (UNC) ya rubuta yadda jaridun ke cigaba da bata daga iyaka zuwa iyaka.

Amma tsaya – Wani haske ne ake hange?

Shafin labarai na hadin gwiwa na farko a kasar ke kokarin fara wani salon samar da labaran a birnin Akron da ke jihar Ohio. The Devil Strip (ko kuma zirin shaidan) – wanda sunan mai jan hankali ya sami asali daga zirin ciyawan da ya raba tsakanin titin mota da ‘yar hanyar simintin da mutane ke tafiya kai a kan hanya – Na bukin cika shekara guda a matsayin ta na jaridar hadin gwiwa, tare da mambobi kusan dubu guda, kuma a cewar mawallafi Chris Horne, har ma sun gota yawan kudaden shigan da su ka yi kiyasin za su samu. Shin wannan zai iya kasancewa alamar cewa jaridun hadin gwiwan za su dore kuma zasu fadada; kuma al’ummomi za su sami karuwa daga jama’an da za su rika samun bayanai nagari wanda zai tabbatar da al’umma mai lafiya?

Tuni an fara yunkurin auna hakan a Northern Carolina, Maryland, Hartford, Connecticut, Pittsburgh, Pennsylvania, Boston, Massachusetts; Springfield Massachusetts; kauyukan Maine da sauransu. Shirin Bayan Project wanda na kafa, shi ne ya fara samar da samfurin labaran dijital na hadin gwiwa a al’umma. Hasali ma yanzu al’ummomi fiye da 40 sun tuntube mu. Kowani shiri na da banbanci: Alal misali, a Boston, burin shi ne samar da majiyar labarai mai nagarta wa al’ummar bakaken fatan da ke da yawan gaske a yankin metro.

Mene ne Labarain Hadin gwiwa ko kuma News Co-ops?

Masu rajin tabbatar da labaran al’umma na hadin gwiwa na ganin wannan salon samar da labaran da suke shiryawa na da babban daman samun nasara a wuraren da shafukan dijital ke fama da rashin karbuwa ko kuma su ke mutuwa, hatta wuraren da ma babu wata majiyar labarai baki daya. Duk da haka dai, har yanzu wannan tsarin bai gama haduwa ba kuma abin da ya ke alkawartawa ba’a riga an sami hujjar yiwuwarsa ba. Kamar kowani irin tsari ko salon a sana’a, wani abu na iya faruwa.

A yanzu haka dai masu shirya wannan tsari na hangen shi daga fannoni daban-daban:

  • Masu karatu, news co-ops cibiyoyin al’umma ne wadanda ke cike gibin bukatun al’umma na labarai da bayanai – yayin da suke kuma bayar da shafukan dijital inda al’umma za ta ga irin martanonin da jama’a ke mayarwa dangane da labarai, har su ma su hada kai a yunkurin da ake yi wajen taimaka ma al’umma. Co-ops su kan shirya duk labarai da ma sauran bayanan da ake bukata kyauta kuma da kan su domin kowa ya karanta.
  • Mawallafa, wannan tsarin na samar da kudaden shiga daga sayar da wani abu mai daraja – kamar damar kasancewa mamba da kuma wani kaso da damar jefa kuri’a a cibiyar da hidima mai mahimmanci kadai ta ke yi wa al’umma ba hatta bayar da murya. Kudaden da ake biya na maye gurbin kudin da ake biya wajen sayen jaridun. Ita dai news co-op burinta shi ne ta baiwa al’umma damar baiwa kansu kyakyawan fata
  • Mambobi, alfunun da za su samu shi ne wani kaso na kamfanin da kuma damar zabe, amma wannan soma tabi ne. Ginshikin shi, shi ne sanin cewa yunkurinsu zai taimaka wajen samar da cibiyar da za ta tabbatar cewa kowa a al’ummar ya san batutuwan da ke da mahimmanci. Banda haka idan aka sami dandali na dijital mambobi na da damar rubuta abubuwa, sa’annan a wasikun da za’a rubuta za’a tambaye su ra’ayoyinsu da abubuwan da suka sani dangane da batu da ma wadanda suke so a wallafa kuma ta yaya za’a wallafa. Wadanda ba mambobi ba basu da wanann damar.
  • Masu abin tallatawa, ma wadanda ke biyan kudi mafi yawa suna samun karin abubuwa kamar sanya sana’ansu a takardar sana’o’i dan kowa ya gani, suna samun ragi idan suna so su yi talla. Kuma ba kaman sauran shafukan intanet ba, za su san wuraren da tallansu zai fita kuma za’a yi komai da nagarta. Za’a sanar da irin alfanun da abin da ake tallatawa ke da shi ga al’umma. Idan har al’umma ta san alfanun shi tabbas zai sami ciniki.
  • Al’umma, labaran za su sanar da masu ‘yancin zabe a al’ummar da duk wani abin da ya kamata su sani, kuma zai basu damar shiga a dama da su irin wanda jaridu da sauran fasahohi ba za su iya ba.

Haka nan kuma doka ta bukaci co-ops su yi jagoranci irin na dimokiradiyya, ta yadda kowani mamba na da kuri’a yin zabe na ‘yan kwamitin zartarwa wadanda za su zaba kuma su sanya ido kan ayyukan edita da babban darekta. Ana iya samun daruruwa ko dubban mambobi ya dai danganta ne da yawan al’umma. Wannan zai raba iko tsakanin mutanen al’umma ta yadda kowa zai sami murya ko kuma karfin fada a ji.

Co-op da ke aiki da kyaua kulluyaumin zai tambayi mambobi ra’ayoyin su ya kuma gayyace su wajen tattauna abubuwan da suka shafe su ko ta hanyar yanan gizo ko kuma ido da ido. Ana kuma iya horas da mutane kan aikin jarida, karatun jarida, da sauran abubuwan da suka shafi ci-gaba. Wannan zai inganta dangantakar da ke tsakanin al’umma. A zamanin da babu aminci sosai da kuma akw samun karancin dangantaka a tsakanin ‘yan al’umma hankulan mutane na komawa ga batutuwan da suka shafi sauran kasashen duniya, rawar da news co-ops na da mahimmancin gaske.

Ga dimokradiyya, akwai dama sosai na samun alfanu musamman idan wannan salon na News co-op ya dore a wuraren da salon aikin jarida na samun riba da na wanda ba ruwan su da riba ba su dore ba. A cikin jaridu fiye da 2100 da suka mutu a 2004 wadanda ake bugawa kowane rana ba su kai 100 ba yawancin su mako-mako ake bugawa. Jaridar UNC da aka ambato a sama ya sami shafuka 525 a matakin al’umma. Wannan adadin ya karu – Cibiyar labarai wadanda ba ruwansu da riba kwanan nan ya bayar da labarin yadda yawan mambobinsu ya karu – amma a daidai lokacin da wannan ke faruwa jaridu fiye da 60 suka mutu.

Co-ops na daukar suffofi daban-daban. News co-ops sun shiga rukunnai daban-daban ke nan kuma wadanda ke cin moriyarsu ke mallakarsu. Yawancin wadanda ke karantawa ne za su mallake co-ops din kamar dai yadda kungiyoyin adashe da na abinci ke yi. Irin wadannan ba su girma sosai amma kuma ana iya daukan darussa daga wurinsu. Kungiyoyin bashi ko Credit Unions misali kanana ne kuma a matsayin masana’anta, kungiyoyin bashi 5,133 da ke kasar na da mambobi milliyan 123.7 wadanda ke da kaddarar da ke da darajar trilliyan $1.79 na dallan Amurka. Wannan ya fi Wells Fargo wanda shi ne banki mafi girma a mataki na uku a Amirka, idan har News co-op suka sami shiga haka, ba karamin riba dimokiradiyya za ta yi ba.

Alfanu da rashin alfanu

To wadanne irin alfanu ne news co-op suke da shi?

Da fatan samun tallafin masu karatu, labaran dijital da suka kafu sukan nemi hanyar hulda domin su ja hankalin masu sha’awan labaran rediyo da talbijin wadanda za su tallafa mu su da kudi. Wadanda ke rajin ganin News Co-op ya habaka suna da ra’ayin cewa kasancewa mamba a irin kungiyoyin ya fi daraja – akwai daidaito, damar zabe, da kuma damar fada a ji a mahimman batutuwan da suka shafi al’umma. Idan har news co-ops suka nuna cewa irin wadannan huldodin su na da mahimmanci za su ja hankalin mambobi kuma idan har suka iya rike su yadda ya kamata, kudaden shiga za su karu. Wanann kudaden da za su samu zai taimaka wajen gudanar da shafukansu da su kansu masu gudanarwar, ko a al’ummomin da ba su da wani arziki sosai irin wadanda suka cika rayuwa babu kafar yada labarai.

Wani karin da za’a samu daga amfani da tsarin co-op din kuma shi ne sahihancin shi. Editoci da manyan darektoci suna karkashin wadanda suka mallaki kamfanin ne dan haka alhakin wadanda suka mallaki co-op din ne su sanya ido a kan editocin da sauransu kuma tunda mambobi ne suka mallaki co-op din, ya zo da sauki ke nan, su ne za su tabbatar cewa editoci da darektoci sun yi abin da al’umma ke so.

Wannan ne abin da ya sa ake ganin tsarin na da sahihanci domin abin da aikin jarida da dimokiradiyya ke bukata ke nan – sahihanci

Mene ne kalubalen wannan tsari da wuraren da ta gaza.

  • Daga farko ana bukatar aiki sosai da kuma mambobin da yawa wadanda za su bayar da kudi mai tsoka wanda za’a yi jari da shi kafin a iya kaddamarwa. Wannan ya fi wahala idan aka kwatanta wanda ya riga ya tara kudi ko. To amma ban da haka, saboda yawan mambobin da akan samu wadanda suka riga suka zuba kudi kuma suna so su ga sun yi riba, da wuya kamfanin ke durkushewa. Haka nan kuma sauya kafar yada labarai na dijital ta zama mallakar al’umma ba wuya sosai, abin da Devil Strip ke yi ke nan.
  • Saboda babu co-op da yawa a sana’o’i, da wuya ake samun wanda ke da kwarewa a fannin, haka nan kuma babu wadanda ke da kwarewa wajen co-op na labarai tunda salon sabo ne. Irin co-op din da aka saba na adashe da sauransu ba su cika hulda da mambobi sosai, kuma nan ne wannan ya bambamta domin shi yana bukatar mambobi. Sai dai kuma a lokaci guda editoci na bukatar yanke shawarwari a wasu fannoni domin tafiyar da komai cikin nasara.
  • Mawallafa a shafukan dijital na fannonin wadanda ke riba da wadanda baruwan su da riba nan da nan ake samun shiga sai dai news co-op yana bukatar matakai da yawa domin ya kunshi neman mambobi, duba ciniki da kuma kiyaye duka abubuwan da ake yi a shafin

Mafi mahimmanci dai shi ne ba’a riga an gama gwada tsarin ba. Akron na jagora kuma yayin da ake samun masu nuna sha’awa a wurare daban-daban, wadanda suka saba sanya kudi a kafofin yada labarai na gargajiya har yanzu ba su kai hankalinsu tsarin news co-op ba.

Tsarin na samun karbuwa

Ba da dadewa news co-ops su ka fara bulla a Amurka ba, amma tun ba yau ba ake da jaridu na kasa mallakar masu karantawa a kasashe irin su Jamus, Italia, Switzerland da Mexico abin da ke nuna ma jama’a cewa mutane za su tallafawa jarida ko kafar yada labaran da za ta biya bukatunsu. A yanzu haka dai akwai sabbin news co-op da suka fara samun tushe a kasashen Canada, Uruguay, da Birtaniya. A Amurka, the Devil Strip ne na farko amma akwai wadanda suka biyo baya:

  • The Devil Strip ya fara ne a matsayin jarida na wata-wata amma sai ya fara fiskantar matsala, sai shugaban kamfanin Chris Horne ya yanke shawarar mayar da shi co-op. Wannan yunkurin ya ya yi sanadiyyar tallafi daga kamfanoni 13 abin da ya kai jimilar rabin milliyan na dallan Amurka daga gidauniyar Knight da sauransu – ya kuma ja hankalin Columbia Journalism Review.
  • The Mendocino Voice wannan shafin intanet ne wanda aka fara 2016, shi ma masu shi sun amince su mayar da shi co-op. A wata hira da Kate Maxwell, mai kamfanin, ta ce an riga an kammala duk wani aikin da doka ta tanada. Shi kan shi wannan shafi ya ja hankalin kamfanoni da masu aikin jarida.
  • Bloc by Block, wanda ke da mazaunin shi a Baltimore na farawa daga farko ke nan domin samar da news co-op di da za ta rika samar da labarai ga al’ummomin Maryland. Kevon Paynter mai kamfanin ya ce burin kamfanin shi ne samar da labarai ta yin amfani da manhajar waya
  • Civic Mind na kokarin kaddamar da wata shafin intanet mai suna Hartford Times, dan ta kasance takwarar wata jaridar da aka rika wallafawa a Hartford na tsawon shekaru 159 kafin aka dakatar a shekarar 1976. Civic Mind ta sami ‘yancin amfani da sunan a hukumance kuma mai kamfanin Thomas Clynch yana aikin kirkiro tsarin da ya dan banbanta daga wanda aka sani – yana son na shi ya kasance wand aba ruwan shi da riba kuma mai kuri’a daya da shugabanci daya.

Shirn Banyan inda na ke aiki, ba co-op ba ne amma yana taimakawa wajen samar da co-op ba tare da yin riba ba. Yana bayar da makaman aiki, da tsari da shwarwarin da za su jagoranci kungiyoyin kauyukan da ke da sha’awan fara amfani da tsarin na co-op. Daga nan Bayan sai ya bas u shafukan da ke da irin abubuwan da suke bukata domin yin nasara. Mutane a jihohi 21 sun riga sun tuntube mu dangane da fara amfani da tsarin na Banyan a yankunansu. Banyan ya sami kyautan kudi kuma yana neman wasu karin hanyoyin samun kudin na shekaru masu yawa domin ya iya daukan ma’aikata ya fara girka ofisoshin news co-op a duk wuaren da ake bukata, inda kuma akwai wadanda za su bayar da kai wajen yin aikin kyauta dan su jagoranci wannan yunkurin. A yanzu haka Banyan na aiki da Civic Mind a Hartford.

A wannan lokacin babu news co-op biyu da ke da kama. Daya ya fara a matsayin mallakar mambobi a Canada amma da ya ke babu kudi daga mambobin sai ya durkushe. Ya yi kokarin samun mambobi daga cikin wadanda ke karantawa amma nan ba ba’a yi nasara ba. Wani kuma a Ingila mai suna Bristol’s Cable ya sauya saboda ya bunkasa har ma ya kara kujeru a kwamitin gudanarwa dan “masu bayar da gudunmawa” The Devil Strip na kwaikwayon wannan tsarin ne. Tsoffin kamfanonin co-op din da aka sani a Turai da Mexico sun fara a matsayin jaridu ne kuma salon aikin su ya banbanta. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata a koya.

Me ya sa yunkurin amfani da sabon salon ke da amfani?

Kusan ko’ina akwai gibi wajen bayar da labaran cikin gida. Dimokiradiyya ba za ta yiwu ba idan babu al’ummar da ta ke da fahimtar al’amurar da ke faruwa kewaye da ita- dan haka wannan gibin na bukatar cikewa.

Shafukan da ke yanar gizo a yanku haka, da na kudi da wadanda ba ruwansu da riba sukan cike wadansu gibin su bar wasu, binciken UNC ya nuna cewa babu daidaito a yanayin da suke bayar da labaran a tsakanin wadanda ke da karfin tattalin arziki. Akwai wadanda za’a iya ware wa, misali, shafukan da ke karban kudi sun fi samun cigaba ne a yankunan da ke da arziki. Shafukan da ba ruwansu da riba kuma sun fi tasiri a birane inda ake yawan bayar da tallafi. Sai dai bayan kwashe shekaru fiye da 10 ana yunkurin kafa su, shafukan da ake da su har yanzu sun gaza maye gurbin jaridun da suke cigaba da durkushewa bare har su shiga yankunan da ba su ma da jaridun samsam.

Akwai shafukan da suka cancanci yabo domin yadda suke aiki a yankunansu. Akwai jaridu wadanda ba ruwansu da riba da suke kawo labaran gwamnati a jihohin Texas da Vermont kuma suna aiki fiye da yadda jaridu ma su ka yi aikin a baya. Jaridun kasa da na duniya baki daya, masu bincike kuma wadanda ba ruwansu da riba musamman ProPublica da Kungiyar hadin-kan ‘yan jarida masu bincike mai zurfi wadanda ke tasanma gwamnati su kuma samu kyauta mai yawa. Wasu shafukan sun taso suna labaran manyan brianen da suka dade ba su da kafofin yada labarai a yankunan da ke kudancin Chicago. Wadannan suna matukar taimakwa dimokiradiyya.

Haka nan kuma a bangaren labarai masu dadi, Hukumar Karbar Haraji na Cikin Gida ko kuma IRS ta fara barin jaridu su sauya daga masu karban kudi zuwa wadanda ba ruwansu da riba. Jaridar Baltimore The Sun na kan hanyar yin hakan. Wannan matakin ma zai taimaka ma jaridun da suka kusan durkushewa su mike. Akwai kuma yunkurin da ake gani na samun tallafi wa kamfanonin jarida na dijital da ake da su yanzu.

Duk da haka dai akwai wuraren da ba’a samun labaran.

“Wannan ne babban kalubalen da aikin jarida ke fiskanta yau” a cewar Martin Baron wanda ya yi ritaya kwanan nan daga mukaminsa na baban darekta a jaridar The Washington Post yayin da ya ke wata hira da PBS News Hour, inda ya kara da cewa “babban barazana ce ga dimokiradiyya kanta”

Wannan lamarin na neman sabbin dabaru. A yanzu haka ana ganin cewa news co-op za ta taka rawar gani.

 

Demonstrating Impact/ Bayyana tasiri

  • Demonstrating Impact: Essential Reading/ Bayyana tasiri: Karatu na musamman
    Links to other sites and other languages
  • Demonstrating Impact: More Reading/ Bayyana tasiri: Karin karatu
    Links to other sites and other languages

 

Tips for Donors/ shawarwari ga masu bayar da tallafin kudi

Tips for Donors/ shawarwari ga masu bayar da tallafin kudi

Ba yau be masu tallafawa aikin jarida suka fara sha’awar labaran da su dadada wa jama’a ba. Jaridun da ke rayuwa kan tallafi kadai irinsu National Geographic da Mother Jones sun yi shekaru gommai ana karantawa. Gidauniyar farko da aka yi dan tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida an kafa ta ne a shekarar 1969 yayin da rediyon kyauta na jama’a a Amirka kuma ya bulla a 1971. Bayan yakin cacar baki, gwamnatocin yamma da gidauniyoyi sun tura billiyoyin dala zuwa kasashen waje domin abun da suka kira “bunkada kafafen yada labarai” wanda zai samar da kafofin yada labarai masu ‘yancin kansu a kasashen da suka daina amfani da salon gurguzu da kasashe masu tasowa.

Sai dai a ‘yan shekarun da suka gabata, da yadda shafukan yanar gizo suka rika daukar labaran karya wanda ya yi sanadiyyar koma bayan da aka samu dangane da ‘yancin fadan albarkacin baki, masu bayar da tallafi sun fara mayar da hankalinsu kan kamfanonin aikin jaridan da ke da ‘yancin kan su. Wannan labari mai dadi ne domin aikin jarida na gaske musamman ma bincike mai zurfi a aikin jarida na matukar bukatar taimako. Alhamdulillah kuma akwai rahotanni da dama da za su iya taimakawa wadanda ke da niyyar bayar da kudi wajen lakantar bayanan abubuwan da faruwa da fagen aikin jaridar a zahiri. Wadannan rahotanni sun duba batutuwan da suka danganci auna tasirin zuba jari a aikin jarida, aiki da kungiyoyin jarida da kuma yadda za’a zabi shirye-shiryen da suka dace.

Kuna iya fada mana idan akwai abubuwan da ku ka gs sun dace mu kara

 

Tallafawa kafafen yada labarai na duniya: Abin da ya kamata masu bayar da tallafi su sani dangane da bayyani, yayi da batutuwan da suka shafi fannin

Wannan rahoron na shekarar 2019 Sarah Amour-Jones da Jessica Clark masu bayar da shawara a Media Impact Funders suka rubuta. Bincikensu ya “yi amfani da bayanai daga taswirar bayanan tallafin kafafen yada labarai, sakamakon binciken manyan kungiyoyin da ke tallafawa shirye-shiryen da ke da dangantaka da kafafen yada labarai a duniya, nazarin bayanai da rahotannin da aka riga aka yi da ma shawarwarin da kwararru suka bayar dangane da abubuwa daban-daban da suka shafi tallafawa kafofin yada labarai.

Mahimman kanu sun hada da:

  • Bayanan da ake da su dangane da tallafawa kafofin yada labarai da bukatar inganta hanyoyin samun bayanai
  • Ra’ayin masu bayar da tallafi dangane da tallafawa kafafen yada labarai da inda suke da damuwa.
  • Bukatar inganta matakan tsaro tsaknin masu kafafen yada labarai da masu tallafa mu su
  • Mahimmancin hadin kan yankuna wajen fadada inganta ‘yancin yada labarai da kafafen yada labarai masu sahihanci da nagarta
  • Kalubalen da kafafen yada labarai masu ‘yancin kan su ke fiskanta a India da Afirka
  • Tsari na musamman na tallafawa aikin jarida a Turai da sauransu.

Aikin Jarida da Fagen Samun Tallafi: Sabbin samfura da kawancen tabbatar da dorewa da bunkasar fagen. Sarah Amour-Jones mai bayar da shawara a kamfanin Media Impact Funders ce ta rubuta wannan rahoton a 2019 wanda ya rubuta yadda tallafi ke cigaba da taka rawar gani wajen tallafawa aikin jarida – Musamman a aikin bincike mai zurfi na cikin gida.

Aikin jarida da hanyoyin samun tallafi ma kafafen yada labarai, wanda Media Impact Funders suka rubuta a shekarar 2018 mai suna. “Abu biyar da ya kamata ku sani da hanyoyi biyar na farawa.” ‘Yar jarida Michele McLellan ce ta rubuta tare da tallafin gidauniyar Wyncote da ke Amirka.

Abubuwan biyar da suka shawarci a sani:

  • Aikin da gidauniyoyi ke so yana fuskantar hadari
  • Wajibi ne aikin jarida ya nemi sabbin hanyoyin kulla dangantaka da al’umma
  • Salon kasuwanci mai dorewa na da mahimmanci sosai
  • Aminci a aikin jarida na fuskantar barazana
  • ‘Yancin kai da gaskiya suna da mahimmanci a aikin jarida

Hanyoyi biyar na faraway:

  • Gano dabarun samun tallafi da zuba jari
  • Tallafawa sabbin dabarun kawo rahotanni, salon kasuwanci da hulda
  • Karfafa kawance da fadada iyaka da yawan wadanda su ke samun labaran
  • Mayar da hankali wajen samun bayanan al’umma
  • Koyon karin abubuwa dangane da samun tallafi

Tasirin bincike mai zurfi: Rahoto dangane da abubuwan koyi wajen auna tasirin bincike mai zurfi a aikin jarida, wanda GIJN ta fitar a shekarar 2017

Domin taimaka ma ma’aikata da masu goyon bayan aikin jaridar da ya tanadi gudanar da bincike mai zurfi, mawallafan sun yi nazarin ra’ayoyi da dama kan yadda ya kamata a auna tasirin bincike mai zurfi a aikin jarida dan ganin yawan shi a zahiri. Sun rawaito cewa “salon da ake amfani da shi wajen tantance yawan ba kai tsaye ya ke kamar yadda ake iya duba yawan mutanen da suka yi amfani da wani shafin yanar gizo ba” sa’annan kuma “tsarin binciken da zai duba ainihin yadda za’a iya auna tasirin bincike mai zurfi bai riga ya nuna ba.”

Ya ce:

Binciken da muka yi ya nuna mana cewa tabbas ana iya auna tasirin bincike mai zurfi kuma albarkacin ya wuce farashin da za’a kashe. Hakika, sau da yawa tasirin shi na da ban mamaki: Falasa masu cin zarafi, shawo kan cin hanci da rashawa, tabbatar da gaskiya, inganta mahimmacin alhakin da ya rataya a kan jama’a da shugabanni da karfafa dimokoradiyya, a ambaci kadan daga cikin gudunmawa masu mahimmancin da ya ke bayarwa – musamman a dimokiradiyya mai tasowa da kasashe masu tattalin arzikin da yanzu su ke bunkasa.

Gabatarwa ga shirin tallafawa aikin jarida da kafofin yada labarai: A shekarar 2018 aka wallafa. Kungiyar Ariadne tare da hadin gwiwar shirin gaskiya da rikon amana suka wallafa a yayin da Sameer Padania ya rubuta. “burin shirin shi ne taimakawa masu zuba jari wajen fadada fahimtarsu dangane da mahimman batutuwa, mahawarori da dabarun bayar da tallafi ga aikin jarida da kafafen yada labarai.

Tallafawa aikin jarida, gano sabbin dabaru: Labaran nasarori da ra’ayoyi na tabbatar da kawance mai dorewa Wannan rahoton na 2018 wanda cibiyar Shorenstein kan kafafen yada labarai, siyasa, da manufofin jama’a a Jami’ar Harvard ta wallafa ya kwatanta misalai ne na irin hadin gwiwar da ke tsakanin masu bayar da kudi da kungiyoyin kafafen yada labarai da ke Amurka.

Masu bayar da tallafin tabbatar da tasirin kafofin yada labarai hadaka ce da ke samun goyon bayan mambobi wadanda ke yunkurin inganta al’umma ta yin amfani da kafafen yada labarai da fasaha. Shafinsu na dauke da cikakken bayani dangane da tushen taswirar tallafawa kafafen yada labarai da ke nuna duk kafafen da ake tallafawa a duk fadin duniya. Akwaibidiyon da ke kwatanta yada za’a iya amfani da hanyoyin bincike masu sarkakiya. Kundin bayanan ya fara ne daga 2009 kuma a kan kara sabbin bayanai a-kai a-kai kuma ana iya samun bayanai har zuwa 2015 da farkon 2018. Masu bayar da kudi na Media Impact sun fitar da rahotanni daban-daban tare da abubuwa biyar da ya kamata a sanin da aka kwatanta daga farko. Rahotannin farko sun hada da:

Ra’ayoyin masu bayar da kudi: Nazarin zuba jari a kafafen yada labarai – Wannan rahoton ya bayyana tushen hanyoyi daban-daban na yin nazarin yadda shirye-shiryen kafafen yada labarai suka yi tasiri kan jama’a

Nazarin tarihin shirye-shiryen labaran da ba ruwan da riba da wadanda ke tallafa musu – wannan shawarwari ne na masu bayar da tallafi da kungiyoyin labaran da ba ruwansu da riba, wadanda ke neman hanyoyin bunkasa dabarun nazarin ayyukan kafafen yada labarai

Bincike mai zurfi a aikin jarida: zai ninka jarin da aka zuba: Bayanin da James Breiner wani mai bayar da shawara kan kafafen yada labarai ya rubuta a 2019

Bincike mai zurfi na aikin jarida a duniya baki daya: Dabarun tallafawa, wani rahoton da aka rubuta a 2013 ma Cibiyar Kasa da Kasa ta Taimakwa Kafafen Yada Labarai lokacin taron Asusun Kyauta na Kasa ga Dimokiradiyya, inda babban darektan GIJN David Kaplan ya duba hanyoyin da za su fi dacewa wajen tallafawa bincike mai zurfi a aikin jarida na kwararru a kasashe masu tasowa da wadanda ke fuskantar sauyi. Wannan ya kunshi tarihin yadda aka fara rahotannin batutuwan da aka yi wa bincike mai zurfi da ma yadda ya yadu a duniya baki daya tare da shawarwari ga hadakar kuniyoyin da ba ruwansu da riba, cibiyoyin rahotanni da na horo

Dabarun hulda da kafafen yada labarai na Dot Connector Studio kan taimaka wa kamfanoni da masu bayar da tallafi su tattauna su samar da dabaru sa’annan su yi nazaribn tasiri. “Zai iya taimakawa wajen nazarin bururruka domin auna alfanunsu da kuma bayyana irin dangantakar da mutun ke so ya kulla da wadanda ke amfani da kafar yada labaran,” a cewar bayanain. Dot Connector Studio kungiya ce mai taimakawa kafafen yada labarai da dabaru. ‘Yar jarida Jessica Clark ta kirkiro kamfanin a 2013. Clark tana kuma bincike a Open Doc Lab da ke cibiyar fasahar da ke jihar Massachusetts.

Gidauniyar Dimokiradiyya ya samar da wata taswirar tsare-tsare dan taimakawa masu bayar da kudi da kungiyoyi wajen fahimtar abubuwan da ke taka rawa wajen labaran cikin gida da shigan jama’a siyasa domin a dama da su, da gano wuraren da ke bukatar taimako.

Hira da Maria Teresa Ronderos, darektan shirin aikin jarida mai zaman kanshi a gidauniyar Open Soceity. A wannan hirar da aka yi a 2018 tace OSF na karkata ga amfani da “tsarun da zai tabbatar cewa kudaden tallafin da za’a bayar sun goyi bayan sabbin dabaru musamman wadanda za’a iya kwaikwaya a yi amfani da su a duk kasashen duniya.” Ta kuma kara da cewa akwai sha’awar irin wadannan tsare-tsaren wadanda “ke ganin kansu a matsayin wadanda ke jagorantar al’ummar mutanen da suke da bayanai da illimi dangane da batutuwa daban-daban.

Raba bayanai da jama’a ta halatattun hanyoyi – Shawarwari kan hanyoyin tattaunawa don masu bayar da tallafi, rahoto ne dangane da binciken da aka wallafa a 2018 wanda kamfanin Ariadne ya gudanar, wanda ya sami tallafin 360 tsakanin watannin Maris da Oktoba

 

This story was originally written by Media Defence/GIJN and published by the Global Investigative Journalism Network.

https://helpdesk.gijn.org/support/solutions/articles/14000036516-sustainability.

Challenges And Solutions For A Free And Credible Electoral Process

Challenges And Solutions For A Free And Credible Electoral Process

The outbreak of COVID-19 has made elections within Nigeria enormously challenging and threatens to overturn other democratic ideals including frequent political dialogues, political party campaigns and manifesto interrogations vis-à-vis active citizen participation across the state[1]. Notwithstanding, the latest challenge of COVID-19 include the several intrigues that come into play seeking to affect the electoral process and its outcomes usually by political agents thereby making it difficult to achieve a free, fair and credible electoral outcome.

Although there have been about six successive general elections in Nigeria, there still exists a couple of bottlenecks in the process of election credibility. The amendment of the Electoral Act has attempted to make provisions for some electronic assistance in the reduction of political agents’ interference. The Independent National Electoral Commission (INEC) has introduced innovations to boost the credibility and trust of Nigerians in the electoral process such as the use of an electronic register of voters, the issuance of a chip-based Permanent Voter’ Card (PVC) to registered voters, and the use of the Smart Card Reader (SCR) for the verification and authentication of voters in 2015[2]. The year 2019 saw the introduction of the Continuous Accreditation and Voting System (CAVS) designed to prevent the possible disenfranchisement of voters, the mandatory use of the SCR for the accreditation of voters, and the discontinuation of the use of Incident Forms to forestall the fraud or abuse by election officials or other stakeholders at the PUs.

The article thus seeks to review some of the challenges and categorize them while proffering solutions for a free and credible electoral process.

Challenges of Electoral Transparency

Despite the aforementioned improvements in the electoral system, elections appear to be losing credibility with the attendant voter apathy[3][4]. The summary of the challenges of the electoral system is categorized thus:

  • Violence and Intimidation[5]: Violent disruptions in the electoral process occasioned by thugs or security forces actions, which either lead to or have the potential of leading to injuries or total/partial stoppage of the process.
  • Voter Inducement: This includes activities that tend to push eligible voters to vote in favour of a particular political party or candidate. This can be monetary, gifts, or “stomach infrastructure” (food supplies given as a bribe to voters to sway the polls).
  • Governance: These are issues that do not have any direct bearing with the election but are brought in because political actors are in power or have connections with people in power.
  • Disenfranchisement: Issues of not being allowed to vote in elections by conscious and concerted efforts by either political thugs, polling unit agents, security forces, or party agents. This category can be on a personal or group basis.
  • Natural Disaster: Incidences that are not man-made but also have adverse effects on the election or electoral process. This includes capsized boats, fire, flood, etc. Such issues can also include pandemics like in the case of the COVID-19. Even when guidelines and regulations[6] are put in place, the voters may still not be able to fully exercise their rights.
  • Intra/Inter-Party Squabbles[7]: Issues of in-fighting within or across political parties. Issues can include counter-accusations, candidacy litigations, or substitution.
  • Result declaration: Attempts to rig or manipulate already announced or yet to be announced results. It also includes results tweeted or tweets about results either through official channels or otherwise. Under this category, it is possible for mischievous elements to try to mislead the public through fake results which then casts doubts in their minds.

Solutions

In planning for a free and credible electoral process, the electoral umpire must be seen to be free and fair even in the build-up to the elections. This is further driven by a lot of voter education which, in the case of Nigeria, appears not to be deliberate considering the dwindling number of voters.

Other proposals include:

More strategic engagement of the various organs of government empowered to conduct citizen education like the National Orientation Agency (NOA), the Federal Ministry of Information and Culture, and the voter education unit of the electoral body. Such engagements should be deliberate and focused on the deployment of various languages and media to reach the grassroot populations.

Establishment of electoral offences commission and enforcement of roles and judgement of same.

To avoid misinformation and disinformation, there is a need for strategic partnership between fact-checking organizations and agencies of government referred to in 1. Fact-checking organizations should be strengthened and non-partisan.

More electoral training on citizen engagement should be done for security operatives and kitted with non-compact gears provided for election purposes.

New Threats to Press Freedom

New Threats to Press Freedom

A PRESENTATION BY GLORIA MABEIAM BALLASON ESQ AT THE 8TH DIGITAL RIGHTS AND INCLUSION FORUM (DRIF) ORGANIZED BY THE PREMIUM TIMES CENTRE FOR INVESTIGATIVE JOURNALISM (PTCIJ) NIGERIA  ON 21 APRIL,2021 AT REIZ CONTINENTAL HOTEL, FCT ABUJA.

Article 19 of the Universal Declaration of Human Rights, Article 10 of the Human Rights Act and Section 39 of the 1999 Constitution of the Federal Republic of Nigeria confer on humans the right to freedom of opinion, expression, the press and the right to receive and impart information and ideas without interference by public authority and regardless of frontiers. This is a qualified right that enables anyone to hold a free opinion and express them verbally, in writing, through television, radio or the internet. Read More

International Forest Day: Group moves to establish Green club in schools in fighting Climate Change

International Forest Day: Group moves to establish Green club in schools in fighting Climate Change

The Premium Times Centre for Investigative Journalism (PTCIJ), through its Agricultural Journalism Project and Natural Resource Program in partnership with Association of flowers Nurseries And Landscaping Practitioners Abuja (AFNALPA), will be embarking on a two-day outreach scheduled to hold from the 20th to 21st of March  2020 to commemorate the International Day of Forests. Read More

FEATURE ON IWD2020 – EQUAL AND INCLUSIVE PORTRAYAL OF WOMEN IN THE MEDIA

FEATURE ON IWD2020 – EQUAL AND INCLUSIVE PORTRAYAL OF WOMEN IN THE MEDIA

The recurring debate about expanding and strengthening women’s voices in the media took on even more significance at the recent commemoration of the 45th International Women’s Day 2020, on March 8, in Abuja. Professional journalists gathered to ask for a minimum industry charter, including policies that will be enforced to address the problem of inequality and imbalance in the media industry and its storytelling.

Read More

AFRICMIL, PT Books, YIAGA Africa, OakTV, Sahara Reporters and TechHerNG launch Sixty Years, Sixty Voices book project

AFRICMIL, PT Books, YIAGA Africa, OakTV, Sahara Reporters and TechHerNG launch Sixty Years, Sixty Voices book project

The African Centre for Media and Information Literacy (AFRICMIL) and its partners — PT Books, YIAGA Africa, OakTV, Sahara Reporters and TechHerNG — on Wednesday 18th March announced a book project to commemorate the 60th anniversary of Nigeria’s political independence. The project involves the production of a book of 60 essays on Nigeria with the title, 60 Years, 60 Voices – Essays on Nigeria at Sixty. Read More

COVID-19 Fact Sheet

COVID-19 Fact Sheet

Coronavirus is a disease that causes damage to the respiratory tract when it is attached to the cells in the lining of the lungs causing damage to it. When the virus enters the body, the patient begins to experience mild symptoms of dry cough, shortness of breath, fever, headache, muscle pain and tiredness compared to ordinary flu. Read More